Wane ne Simon Ekpa, ɗan Najeriya da Finland ta kama bisa zargin ta'addanci? - BBC News Hausa (2024)

Wane ne Simon Ekpa, ɗan Najeriya da Finland ta kama bisa zargin ta'addanci? - BBC News Hausa (1)

Asalin hoton, Simon Ekpa/Twitter

Cif Aliyu Umar masanin tsaro a birnin Kaduna ya ce kama Simon Ekpa zai taimaka wajen karya gwiwar magoya bayansa.

Sai dai ya ce wannan ne lokacin da ya dace gwamnati ta karya lagonsa ta hanyar ɗaukar matakin da ya dacewa a kan magoya bayan nasa.

"Duk inda aka kama shugaba to magoya bayansa za su wargaje saboda haka gwamnati ta je ta bi su har su nemi sulhu da gwamnati. Shi dama Simon Ekpa ai ba shi da tasiri da yawan magoya bayan Nnamdi Kanu. Shi ma mabiyin Nnamdi Kanu ne". In ji Cif Aliyu.

Dangane kuma da ko akwai yiwuwar mayar da Simon Ekpa Najeriya, masanin ya ce "idan dai har ana so kamun jagoran ƴan awaren ya yi tasiri to dole ne a mayar da shi Najeriya domin ya fuskanci hukunci."

Masanin ya kuma ce yana ganin dalilin da ya sa Finland ta sauya matsayinta kan Simon Ekpa saɓanin a baya shi ne "sun fahimci cewa idan ya gama ruguza Najeriya to zai koma kan Finland ɗin tun yana da takardun zama ɗan ƙasa guda biyu." Kamar yadda Cif Aliyu ya yi ƙarin haske.

Na yi farin ciki da kama Simon Ekpa - CG Musa

Wane ne Simon Ekpa, ɗan Najeriya da Finland ta kama bisa zargin ta'addanci? - BBC News Hausa (2)

Asalin hoton, DHQ/SIMON EKPA/X

Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa ya ce ya yi fari ciki da kamen da hukumomin Finland suka yi wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware ta IPOB ta Najeriya, Simon Ekpa.

Cikin wani saƙo da kakakin ma'aikata tsaron ƙasar, Manjo Janar Tukur Gusau ya aike wa BBC ya ce babban hafsan tsaron ƙasar ya ce yana fatan kamen ya zama wani mataki na tisa ƙeyar Mista ekpa zuwa Najeriya don ya fuskanci shari'a.

A ranar Alhamsi ne hukumomin Finland suka kama Simon Ekpa tare da aika shi gidan yarin ƙasar, bayan gurfanar da shi a kotu, kan zargin tunzura mutane su aikata ayyukan ta'addanci.

Kotun ta ce ta samu Simon Ekpa ne da laifin yaɗa aƙidu na ƴan aware a kafar sada zumunta, a ranar 23 ga watan Agustan 2021 a birnin Lahti na ƙasar ta Finland.

A watan Yunin wannan shekarar ne babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Chiristpher Musa, ya zargi gwamnatin ƙasar Finland da bai wa Simon Ekpa mafaka inda ya yi kira ga Najeriya da ta bi hanyoyin diflomasiyya domin tabbatar da kama jagoran na ƴan aware.

“Mun sha yin ƙorafi dangane da batun Simon Ekpa. Yana Finland kuma gwamnatin Finland na ba su mafaka." In ji Musa.

Wane ne Simon Ekpa da gwamnatin Finland ta kama bisa zargin ta'addanci?

Simon Ekpa shugaban haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware ta IPOB a Najeriya ya tsinci kansa a gidan yarin ƙasar Finland bisa tuhumar zargin aikata ayyukan ta'addanci.

Kafafen watsa labaran ƙasar ta Finland sun ce kotun lardin Paijat-Hame ce ta aike da Simon Ekpa zuwa gidan yarin bisa tuhumar tunzura mutane su aikata ayyukan ta'addanci.

Kotun ta ce ta samu Simon Ekpa ne da laifin watsa aƙidu na ƴan aware a kafar sada zumunta, a ranar 23 ga watan Agustan 2021 a birnin Lahti na ƙasar ta Finland.

Hukumar da ke binciken laifuka ta ƙasar Finland ɗn ita ma ta bayar da sammacin kama wasu ƙarin mutum huɗu bisa zargin ayyukan ta'addanci.

Ekpa wanda ɗan ƙasar Finland ne wanda kuma aka haife shi a shekarar 1985 ya fara bayyana cewa yana goyon bayan ƙungiyar ƴan aware ta IPOB da ke Najeriya.

Ƴansanda sun ce suna zargin Ekpa ne da yaɗa tarzoma da ayyukan batagari a kudu maso gabashin Najeriya.

A 2023, lokacin babban zaɓen Najeriya, a wani bidiyo da ya wallafa a ashafinsa na kafar sada zumunta ya ayyana cewa ba za a yi zaɓe ba a yankin kudu maso gabashin Najeriyar ba inda ya gargaɗi al'ummar yankin da ka da su kuskura su shiga zaɓen.

Simon Ekpa da mutane huɗun da hukumar binciken laifuka ta nemi a kama dukkan su na tsare.

Yayin da shi Simon Ekpa yake mazaunin birnin Lahti, biyu daga ciki mutane huɗun da su ma aka kama na zaune ne a Helsinki, inda kuma ba a samu sunan ɗaya daga cikin huɗun ba a rijistar jama'ar ƙasar ba.

Wannan ne dai karo na biyu da hukumomi a Finland ke kama Simon Ekpa. Kamun na yanzu dai da alama ya sha banban da na baya inda aka kama shi kuma aka sake shi. Ba a san inda wannan sabuwar tuhumar za ta ƙare ba.

A baya dai kamun da aka yi Simon Ekpa na da alƙa ne kawai da laifi guda ɗaya.

A 2023, hukumar binciken laifuka a Finland ɗin dai ta tsare Ekpa bisa laifin karɓar kuɗaɗe ba bisa ka'ida ba. Ƴansanda sun sake shi daga baya bayan tarewar ta wani ɗan lokaci.

Me Simon Ekpa ke yi?

Simon Ekpa dai ya kasance ɗan ɗan asalin Najeriya mazaunin ƙasar Finland da ya ayyana kansa a matsayin magoyi bayan shugaban ƴan aware na Biafra da ke Najeriya, Nnamdi Kanu.

Ekpa da ke zaune a Finland dai na fafutukar ganin yankin kudu maso gabashin Najeriya ya bangare domin cin gashin kansa mai suna Jamhuriyar Biafra ko kuma Biafran Republic.

Simon Ekpa wanda ke da mabiya fiye da 60,000 a kafar X inda nan ne ɗaya daga cikin dandalin da ke amfani wajen yaɗa manufofin aƙidar aware ta Biafra, yana ayyana kansa ne a matsayin mai rajin kare haƙkin ɗan'adam kuma shugaban kamfanin lauyoyi na Ekpa & Co Oy, sannan kuma mai bincike kan harkokin shari'a.

Ekpa yana kuma ayyana kansa a matsayin ɗan siyasar ƙsar Finland sannan kuma kakakin ƙungiyar ƴan awaren Biafra.

Wane ne Simon Ekpa, ɗan Najeriya da Finland ta kama bisa zargin ta'addanci? - BBC News Hausa (2024)
Top Articles
Latest Posts
Recommended Articles
Article information

Author: Terence Hammes MD

Last Updated:

Views: 6043

Rating: 4.9 / 5 (69 voted)

Reviews: 84% of readers found this page helpful

Author information

Name: Terence Hammes MD

Birthday: 1992-04-11

Address: Suite 408 9446 Mercy Mews, West Roxie, CT 04904

Phone: +50312511349175

Job: Product Consulting Liaison

Hobby: Jogging, Motor sports, Nordic skating, Jigsaw puzzles, Bird watching, Nordic skating, Sculpting

Introduction: My name is Terence Hammes MD, I am a inexpensive, energetic, jolly, faithful, cheerful, proud, rich person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.